Takaddama ta kaure tsakanin gwamnatin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo da kasar Rwanda, bayan kaiwa wani jirgin yaki kirar Sukhoi-25 hari, yayin da yake kokarin sauka bayan barin sa Congo.
Musayar yawun da sassan biyu suka yi a jiya Talata, ita ce ta baya bayan nan tsakanin makwaftan biyu, wadanda dangantakarsu ta tabarbare sakamakon ayyukan ‘yan tawaye.
Cikin wata sanarwa, kakakin gwamnatin Congo Patrick Muyaya, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa jirgin yakin kasarsa, yana mai watsi da zargin da gwamnatin Rwanda ta yi, cewa jirgin yakin ya kutsa yankin makwafciyar ta su.
Kafin hakan a ranar Talata, Rwanda ta zargin jigin yakin Congo da yin kutse cikin sararin samaniyar ta har sau 3, wanda hakan ya tilasa mata daukar abun da ta kira da “matakin kare kai”.
Zaman doya da manja na kara ta’azzara tsakanin sassan 2, tun bayan da aka sake komawa fagen daga, tsakanin mayakan ‘yan tawaye na M23, da dakarun gwamnatin janhuriyar dimokaradiyyar Congo a arewacin Kivu.
Congo dai na zargin Rwanda da goyawa mayakan na M23 baya, duk da cewa Rwanda ta sha musanta hakan