Sojojin kasar China sun fara atisaye mafi girma a yankin Taiwan, a wani mataki na nuna karfin tuwo kan muhimman hanyoyin jiragen ruwa na kasa da kasa, bayan ziyarar da shugabar majalisar dokokin Amurka, Nancy Pelosi ta kai tsibirin.
Pelosi ta bar Taiwan ne a ranar Laraba bayan ziyarar da ta bijirewa jerin barazanar da China ta rika yi, wanda ke kallon tsibirin mai cin gashin kansa a matsayin yankinta.
Pelosi wadda ta kasance mai mukami mafi girma daga Amurka da ta ziyarci Taiwan cikin shekaru 25, ta sha alwashin ba za su yi watsi da yankin da su ke dauka a matsayin mai muhimmanci ba wajen karfafa dimokaradiyya.
Wadannan kalamai ne suka kara fusata China, wadda ta yi alkawarin mayar da martani tsattsaura tare da sanar da fara atisayen soji a ‘iyakokin ruwan tsibirin na Taiwan.
Dakarun na China sun fara atisayen ne, da misalin karfe 12 na daren jiya laraba, ba kuma tare da bata lokaci ba suka fara gwajin harba manyan makamai, a wasu yankuna 6 da ke zagaye da tsibirin na Taiwan, masu nisan kilomita 20 kacal daga ainahin cikin gari, atisayen da ba zai kare ba sai a ranar lahadi mai zuwa.
Ma’aikatar tsaron Taiwan ta ce ta na sa ido sosai kan atisayen na sojojin China, kuma tsibirin a shirye yake don tunkarar yaki, amma ba za ta fara takalo shi ba.