Zafafan martani da shaguɓe iri-iri na ci gaba da biyo bayan matakin gwamnatin Najeriya na tallafa wa maƙwabciyarta Nijar da motocin da suka kai darajar kusan naira biliyan ɗaya da rabi.
Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta bai wa maƙwabciyar tata motocin 10 da zimmar inganta ayyukan tsaro ne.
Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriyar ke tsaka da nata matsalolin tsaron a kusan kowane saƙo.
Ministar Kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed, ta faɗa wa manema labarai ranar Laraba cewa “an ɗauki matakin ne saboda taimaka wa Nijar ta inganta tsaron iyakarta da Najeriya”.
Ƙasashen biyu da kuma Kamaru da Chadi, sun haɗa iyaka a tsakaninsu mai girma sosai kuma dukkansu na fuskantar hare-haren ƙungiyar Boko Haram da sauran masu iƙirarin jihadi.
A cewar ministar: “An ɗauki lokaci Najeriya tana tallafa wa makwabtanta, musamman ma mafiya kusanci da nufin karfafa su domin su kare kasashensu ta bangaren da ka iya shafar mu.
“Kuma ba wannan ne karon farko da Najeriya ta taimaka wa Nijar ko Kamaru ko Chadi ba.”
Binciken da sahin BBC Hausa ya gudanar ya nuna cewa ba wannan ne karon Farko da Najeriya ta fara taimaka wa maƙwabtan nata ba kamar yadda Minista Zainab ta faɗa, amma a yanzu ne abin ya fi fitowa fili.