Jami’an tsaro a jihar Virginia ta kasar Amurka sun tabbatar da yadda wani dalibi mai shekaru 6 a duniya ya harbi malamarsa tare da ji mata mummunan rauni bayan ta bata masa rai a lokacin da ta ke basu darasi a makaranta.
Jaridun kasar sun ruwaito cewa an yi nasarar ceto ran malamar ne bayan kai mata dauki gaggawa ko da ya ke har yanzu ta na dakin kula da marasa lafiyan da ke cikin matsanancin hali.
Jami’an ‘yansandan jihar sun tabbatar da faruwar lamarin sai dai basu yi karin bayani kan dalilin da ya haddasa harbin malamar ba.
A cewar ‘yan sandan dalibin mai shekaru 6 a duniya ya shiga makarantar ne da bindiga kuma suna kan bincike don gano daga inda bindigar ta fito.
Harbe-harbe a makarantun kasar Amurka ba sabon abu ba ne sai dai shigar yaron mai shekaru 6 da bindiga makaranta shi ne lamari mafi daure kai ga jami’an yan sandan jihar ta Virginia.