Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a girgizar kasa masu karfin awo 7.7 da 7.6 da suka afku a Kahramanmaras ya karu zuwa dubu 12 da 873.
Ma’aikatar Bayar da Agajin Gaggawa ta Türkiye ta sanar da cewa sakamakon girgizar kasar da ta afku a ranar 6 ga watan Fabrairu, asarar rayuka a yankin da bala’in ya shafa ya karu zuwa dubu 12 da 873 sannan adadin wadanda suka jikkata ya kai dubu 62 da 937.
Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto a baraguzan gine-gine dubu 6 da 444 da suka lalace.
Ma’aikata dubu 113 da 201 ne ke aiki a yankin, ciki har da masu aikin bincike da ceto.
An kafa tantuna dubu 73 da 11 daga cikin tantuna dubu 94 da aka aike zuwa yankin.
An kuma aike motoci dauke da dakunan dafa abinci 95, motocin abinci 79, ma’ajiyar abinci 1, karafunan da ake dafa abinci a ciki 4, dakunan dafa na wucin gadi 39, kwantena 1 da motocin raba abinci 86 zuwa yankin.