Matar Gida : tare da Khadija Salisu Danmaliki
YADDA AKE FUNKASO
Kayan hadi da ake bukata
1. Alkama kamar (gwangwani hudu ) .
2. Fulawa kamar ( gwangwani daya ).
3. Ruwan Tsamiya ( rabin gwangwani ).
4. Yeast( cokalin shayi kada ya cika sosai ).
5. Sikari ( cokali daya )
6. Ruwan Kanwa ( cokali daya ).
7.Man suya ( Kwalba daya ).
YADDA ZAKI HADA
Uwar gida bayan kin tanadi duk kayan hadin da muka lissafa abaya, sai ki sami robar ki mai murfi ki zuba Sikari da Yeast da Ruwan Tsyamiya dana Kwanwa kamar yadda muka auna wa uwar gida Fulawar ki sai ki hada ta da garin Alkamar ki, da zarar Yeast din ki ya narke sai ki juye Fulawar ki, ki kwaba ta sosai ki tabbatar babu gudaji a ciki, san nan karki bari kwabin na ki yayi ruwa kuma kada yayi tauri sosai, sai ki rufe robar ta ki ta samu kamar Awa daya.
Bayan Awa daya Uwar gida sai ki bude zakiga Fulawar ta tashi sosai, sai ki dora Man ki a kan wuta yayi zabi sosai sai ki kara kwaba Fuwarki zakiga ta koma kasa ta kwanta, kuma zakiga a yayin da kika dada juyashi kwabin zai dada sakin jikin sa sosai.
Bayan haka Uwar gida, sai ki sami Farantin ki mai tsafta, sai ki rika gutsurar kullun kina dora wa akan Farantin sai ki huda tsakiyar kullun akan Farantin sai ki saka a cikin Mai a hankali zakiga yana kunbura a cikin Man a kan wuta.
A binda lura ga Uwar gida shine, Funkaso baya son yawan juyawa a cikin Mai, sai dai ki raka kula idan kinga kasan sa ya soyu sai ki juya saman shima ya soyu, san nan Funkaso yana bukatar wadataccen Mai wajen Suya san nan amfanin Tsamiya da muka saka zata hana shi shan mai wajen Suya kuma zata taimaka wajen gyara Suyan yayi Ja sosai gwanin Sha’awa.
Shikenan Uwar gida an kammala, adadin yawan Funkaso a dadin yawan kayan hadi.
Edited by Kabiru A.Dukawa