A wani mataki na tsaurara yaki da yan taadda gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da dokar hana amfani da mashina masu kafa biyu
Kawo Yanzu Alummar jhar na ci gaba da tsokaci tun bayan ɓullo da sabbin matakan zafafa na yaƙi da ‘yan fashin daji da Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya yi.
Cikin matakan har da ƙaddamar da rundunar jami’an tsare garuruwa da sabbin baburan aiki 1,500 da motoci guda 20, baya ga ɓullo da matakin taƙaita hawa babura da dare a wasu unguwannin birnin Gusau.
Gwamnati dai ta ba da umarnin cewa duk mutumin da aka gani daga ƙarfe takwas na dare zuwa safiya, a harbe shi.
Mahukuntan jihar ta Zamfara sun ce sun dauki mataki kan hana zirga-zirgar babura ne bayan an lura cewa wasu miyagu na aikata laifuka a kewayen birnin Gusau, kamar su Mareri da Barakallahu da Janyau ta Gabas da Tsauni da Siname da Gada Biyu da Samaru da Damba.
Gwamnatin jihar ta ce wannan lamarin na iya zama babbar matsalar tsaro, kamar yadda Ibrahim Dosara, kwamishinan yada labarai na jihar ya shaida wa BBC.
“Wannan ne yasa hukumar tsaro ta jihar ta amince da a dauki wannan matakin na hana hawan babura daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe, domin a wannan lokacin ne a ke amfani da babura ana aikata laifuka.”
Kwamishinan ya ce idan aka tsayar da mai babur domin a bincike shi kuma bai tsaya ba, to ya tabbatar yana cikin ‘yan ta’adda kuma nan take za a iya harbe shi.