Alkaluman da AFP ya tattara na nuna cewa ana kashe mutum 111 kowacce rana a sassan kasar ta Amurka, wanda ya mayar da jumullar mutanen da ke rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren bindigan zuwa dubu 41 kowacce shekara.
A cewar kungiyar Everytown zuwa yanzu makamantan hare-haren ‘yan bindiga dadi ya karade ko’ina a sassan Amurka inda a jihar Texas da ke da kwarya-kwaryar dokar sayar da makamai ke ganin mutuwar mutane akalla dubu 3 da 600 duk shekara sanadiyar harin bindigar.
Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu akalla mutane dubu 17 da 199 hare-haren bindigar ya yi sanadin mutuwarsu ciki har da dalibai yara 19 da malamansu 2 da wani dan bindiga ya harbe a wata makarantar firamare da ke jihar Texas a jiya laraba.