Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni ya zargi bankin duniya da yunƙurin jefa ƙasar sa cikin ƙangin tattalin arziki saboda dokar da ta samar kan auren jinsi.
Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da bankin ya fitar cewa zai dakatar da bai wa ƙasar bashi saboda rashin goyon bayan auren jinsi guda, wanda ya saɓa tanadin bankin.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar a kafar sada zumunta, shugaba Museveni ya ce “Uganda za ta samu bunƙasa ko tana samun bashi ko bata samu”.
Ya ce abin takaici ne yadda bankin ke neman ”tilasta mana yin watsi da al’ada da addininmu da kuma abubuwan da muka yarda da su don kawai mu samu kuɗi”
A cikin watan Mayu shugaba Museveni ya sanya hannu kan dokar haramta auren jinsi wadda ta yi tanadin hukuncin kisa da ɗaurin shekara 20 ga ƴan luwaɗi da maɗigo.
Bankin duniya ya bi sahun Amurka wajen ƙaƙabawa Uganda takunkumi saboda matsayar ta kan auren jinsi ɗaya.