Kungiyar Tarayyar Turai ta bayyana shirin ta na janye wani adadin na jami’anta da ke aikin bayar da horo ga sojojin kasar Mali, wanda hakan ke alamta cewa alaka na ci gaba da yin tsami tsakanin kasashen na Turai da kuma gwamnatin mulkin sojin Mali.
Shugaban ofishin kare manufofin ketare na Tarayyar Turai Joseph Borrell, shi ya bayyana wannan mataki, a lokacin da yake gabatar da jawabi ga ministocin tsaron yankin wadanda ke taro a birnin Brussels.
To sai dai Borrell ya ce duk da haka, kungiyar za ta ci gaba da kasancewa a kasar ta Mali, inda ya ce tuni ya samu tabbaci daga Spain wadda ta fi kowace kasa yawan sojoji a Mali cewa ba za ta rage adadinsu ba, yayin da Jamus ta ce za ta kwashe mafi yawan nata dakarun daga Mali zuwa makociyarta Jamhuriyar Nijar.
A cikin watan afrilun da ya gabata ne kungiyar ta EU ta sanar da cewa ta dakatar da aikin bayar da horo ga jami’an tsaron Mali bayan da kasar ta gayyaci sojin haya na Wagner daga Rasha don taya ta yajki da ayyukan ta’addanci.
A nata bangare kuwa, ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta bayyana matakin da gwamnatin mulkin sojin Mali ta dauka na ficewa daga kawance G5-Sahel mai fada da ayyukan ta’addanci a matsayin wanda zai kara mayar da kasar a matsayin saniyar ware.