Rundunar sojin Najeriya ta yi watsi da wani zargi na cin hanci da rashawa da wasu sojojin kasar suke yi wa manyansu.
Sojojin sun yi kukan cewa manyansu na cinye musu kudadensu na alawus, inda suka bukaci shugaba Buhari ya dauki mataki a kai, idan ba haka ba za su yi bore.
Rundunar sojin ta bayyana cewa tana aiki ne da tsarin biyan albashi na bai-daya ta intanet da gwamnati ta fito da shi, kuma abin da take yi bashi da bambanci da wanda takwarorinta, da sojin sama da na ruwa ke yi, don haka a cewar rundunar babu yadda za a zalunci wani a karkashin tsarin.
Wani abin da rundunar ta ce yana da tayar da hankali shi ne barazanar da kananan sojojin suka yi cewa za su yi yajin aiki idan ba a biya su hakkokinsu ba, alhali a irin wannan yajin aikin a aikin damara tamkar tawaye ne ko bore ga kasa.
Wata sanarwar da daraktan hulda da jama`a na sojin kasan Najeriya, Birgediya-janar Onyema Nwachukwu ya sanya wa hannu ta ce zargin da sojojin ke yi ya nuna cewa sun jahilci yadda soji ke tafiyar da harkar kudi.
Ya tabbatar da cewa ana zargin ne da nufin bata wa sojin kasa suna tare da sanyaya gwiwar dakarunta, wadanda ta ce sabon Hafsansu ya dawo da armashi da karsashin aikin a zukatan zaratan kasar sakamakon yadda ake biya musu hakkokinsu.
Kazalika rundunar ta lura cewa sojojin sun yi zargin ne a cikin wata kurmar wasika, wadda suka aike wa shugaba Buhari ba tare da an rubuta sunayen masu ita ba, wadda hakan a cewar rundunar alama ce ta rashin gaskiya.
Amma duk da haka, rundunar sojin ta ce za ta gudanar da bincike a kan lamarin.
Kananan Sojojin dai sun rubuta budaddiyyar wasika ne zuwa ga shugaba Buhari, wadda a ciki suka zargi manyan sojin Najeriya da yi musu kwange, kuma sun kwana biyu suna kokawa amma shugaban kasar da sauran wadanda abin ya shafa basu ce komi ba.
A cikin wasikar, sojojin suka ce kudadensu na alawus daban-daban ba sa shiga hannunsu…har ta kai ga su suke kukutawa su saya wa kansu takalma da sauran kayan damara.
Sojojin sun bayyana cewa duk da cewa wasu na raina su ba don sadaukar da rayukansu da suke yi ba da komai ya cije a Najeriya.
Sun yi gargadin cewa idan tura ta kai bango, har suka yi tawaye, to manyan sojojin da suke musu cogen za su rasa inda za su sa kansu da ƴaƴansu.
Haka kuma za su rasa inda za su tsuguna su ci abin da suka tara. Sannan za su rasa hanyar da za su fice daga Najeriya.
Babu wani martanin da ya fito daga fadar shugaban Najeriya dangane da wannan budaddiyar wasikar.