Mutane 10 sun shiga hanu bisa Zargin juyin mulki a kasar Mali.

Rundunar  sojin kasar Mali  ta sanar da kama mutane 10, yayin da gwamnati tace ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin domin gano sauran wadanda suke da hannu a yunkurin juyin mulki a kasar.

Kamfanin dillancin labarai na Faransa yace babu wata alama dake nuna yunkurin a makon jiya har sai lokacin da aka gabatar da sanarwar.

Kasar Mali ta gamu da juyin mulkin sau 2 tun daga watan Agustan shekarar 2020 lokacin da sojoji suka kawar da gwamnatin zababben shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Kasar ta kwashe shekaru tana yaki da mayakan dake ikrarin jihadi dake kuma alaka da kungiyar Al Qaeda da IS, rikicin da ya bazu zuwa kasashen Nijar da Burkina Faso dake makotaka da ita.

Sojojin dake mulki a kasar sun katse hulda da kasar Faransa da ta yiwa Mali mulkin mallaka, yayin da suka rungumi Rasha wajen yaki da Yan ta’adda.

Gwamnatin sojin dake mulki tayi alkawarin mayar da mulki ga fararen hula a watan Fabararirun shekarar 2022 amma kuma daga bisani sai ta sake matsayin ta, abinda ya janyo mata suka daga kungiyar ECOWAS da AU da Majalisar Dinkin Duniya.

Wata sanarwar da gwamnatin sojin ta karanta ta kafar talabijin din kasar tace wata kungiyar bata garin hafsoshin sojoji da jami’an su tayi yunkurin juyin mulki a daren 11 zuwa 12 ga watan Mayu na wannan shekara ta 2022 amma kuma ba suyi nasara ba

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments