A Daren jiya Asabar ne Zababben Dan Majalissar Jiha Mai Wakiltar karamar Jama’are Karkashin Inuwar Jam’iyyar NNPP Hon. Mubarak Haruna, Yakai was jagoran jam’iyar su na kasa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Ziyarar Neman tabarraki.
Hon. Mubarak Haruna Mairakumi, ya gabatar wa da kwankwaso takardar shaidar lashe Zabensa da hukumar Zabe mai zaman kanta ta bashi.
Jagoran jam’iyar NNPP na kasa yayi wa Matashin Dan Majalissar Addu’a tare da sanya Albarka a gare shi kuma ya ja hankalin sa da ya kasance Walkili Nagari. Domin Al-ummar sa, Suyi Alfahari Dashi..