Ya’yan wasu jigajigan jam’iyar APC sunziyarci Sanata injiya Dacta Rabiu Musa Kwankwaso.
Hon. Bashir El-Rufai Ya Jagoranci Abokansa Inda Suka Kaiwa sanata Rabiu Musa Kwankwaso Ziyara. Cikin Wannan Dare.
Dan gwamnan jihar Kaduna kuma Zababben Dan Majalissar tarayya na karamar hukumar Kaduna ta, Arewa Hon. Bashir. El-Rufai. tare da, Abokansa Mahamud Nuhu Ribadu. Da Mustapha Isma’il da kuma, Al’amin Nasidi. Sun kaiwa Jagoran Jam’iyyar NNPP na kasa. Sen. Rabi’u Musa Kwankwaso Ziyarar Gaisuwar bangirma.
Idan Baku manta ba kwanakin baya Zababben Dan Majalissar ya bayyana Cewa Duk da Mahaifin sa gwamna ne A jihar Kaduna kuma Dan Jam’iyyar APC ne amma tsarin Siyasar Kwankwaso tana burge shi.
Wadanda suka kai ziyarar ta barka da shan ruwa ga Madugun siyasar Arewa da suka hadar da Bashir Nasiru El-Rufai da Mahmud Nuhu Ribadu Dakuma Al-amin Nasidi.da Mustapha Ismail sun yaba da salon siyasar Madugun.