Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara shida

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Nasarawa, ta tabbatar da sace wasu yara ’yan makaranta shida, yayin da suke kan hanyar su ta zuwa makaranta a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ramhan Nansel, ya shaidawa manema labarai a Lafiya babban birnin jihar cewa, yaran dalibai ne na wata makarantar firamare ta gwamnati, ‘yan shekaru tsakanin 7 zuwa 8. Kuma wasu ‘yan bindiga akan babura, da ba a san su ba  suka sace su a garin  Alwaza, na Jihar da safiyar Jiya Juma’a.

Ramhan Nansel, ya kara da cewa, ‘yan sanda sun gana da shugabancin makarantar da iyayen yaran, kuma sun tura wani ayarin jami’an tsaro na hadin gwiwa zuwa yankin, domin lalubowa da ceto yaran, yana mai cewa sun fara farautar bata garin.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ba ‘yan sanda duk wasu bayanai da za su taimaka wajen ceto yaran da cafke wadanda suka sace su.

 

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments