Yan sanda sun cafke wasu Yan tada zaune tsaye 61 a jihar Kano.
A kokarin na tsaftace jihar daga ayyukan Daba da bangar siyasa rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta kame wasu zaratan batagari guda 61
Kwamishinan yan sanda na jihar, Mamman Dauda, shine ya bayyana hakan a wani jawabi da yayi wa manema labarai ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano Abdullahi Haruna kyawa.
Dauda yace Kamen ya biyo bayan umarnin babban sifetan yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba, da ya baiwa kwamishinonin sa na jihohi na kowannan su ya tabbatar da ya kawo zaman lafiya a jihar sa.
Ya kara da cewa an Sami wu kake 33 da gatura hudu da almukusa da ku sinki-sinkin kayan maye.
Kazalika yace rundunar su Ba za ta yi kasa a guywa ba wajan gurfanar da wadanda suka shiga hannun rundunar su ba a gaban kotu.