Anyi kira ga matasa da su riki rubuce- rubuce a matsayin wani jigo na inganta rayuwarsu da bunkasa Ilminsu.
Kwamishinar cigaban mata da walwalar jama ‘a ta jihar Kano, Dakta .Zahra,u Muhammad Umar ce ta bayyana hakan yayin kaddamar da littattafan Adabin larabci Wadan Nasir Almalikiy Aliyyul-khawwas Shaikh Nasir kabara ya wallafa .
Taro ya gudana ne a dakin taro na Makarantar koyon harkokin Shari,a ta Kano (Legal).
Dakta Zahra,u muhd umarta bayyana ilmin larabci a matsayin wata hanya da ke bunkasa addini. Ta kuma yabawa Marubucin bisa jajircewarsa a matsayinsa na Wanda bai haura shekaru ashirin da biyar (25)ba ya rubuta littafai kusan guda Dari(100).
Dr Zah’ra’u muhd Umar ta yi kira ga iyaye da su nunawa ya’yansu muhimmancin da ke akwai wajen yin bincike na ilmi ,acewarta hakan zai karawa matasan sha,awar yin rubuce-Rubuce.
Taro ya samu halartar manya masana a harkar ilimi,daktoci,da masu rike da sarauta gargajiya da yan kasuwa da
Yan’ siyasa.jami’ar hulda da jama”a ta ma”aikatar mata Bahijja Malam kabara ta kara da cewa kwamishinar tayi bayani mai tsawo akan rungumar dabi’ar rubuce rubuce ga matasan..