Daga jamila sulaiman Aliyu.
Hukumar hisbah taja hankalin ma’aurata dasu zage damtse wajen gudanar da ma’amalarsu daidai da yadda addini ya tsara ko don tarbiyya ya’yansu ta inganta.
Maitaimakiyar kwamandan hisbah ta karamar hukumar nassarawa malama Wasila Abdullahi ce ta bayyana akan a yayin da takai ziyar fadakarwa ga mata a mazabar Tokarawa dake karamar hukumar nassarawa ta yi lacca mai ratsa jiki tare da nusar da matan irin dabi,un da suka kamata su runguma a gidajen auren su ta hanyar da zasuyi hannun riga da shaidan tare da samun karuwar arziki a gidajen su.
Malama Wasila Abdullahi ta bayyana matsalolin da suka kamata mazaje su gyara da cewa sauke nauyin iyali shine sahun farko da kuma yiwa iyalin raha,barkwanci da kuma saurarensu aduk lokacin da bukatar hakan ta taso, sa,ilin nan su kuma matan su kaucewa cin amanar aure ta hanyar rage kudin cefane da koyawa ya’ya roko da yawo da gulma da annamimanci da boye alkhairin miji ko abokiyar zama da makwafta da kuma tona asirin ya’yan mutane domin yin hakan ka iya rusawa kowannensu farin cikinsa
.kwamandiyar Nassarawa ta ce wannan lacca sun farotane tun daga matakin makarantu har zuwa unguwanni domin sauran yan’uwa maza da mata su gyara dabi’unsu domin shine tushen kafa hukumar ta hisbah ma,ana horo da kyakykyawa da hani da mummuna.
Malama Wasila Abdullahi tasha alwashin karade fadin karamar hukumar ta nassarawa baki daya.