Harin ya tarwatsa wasu kauyuka da dama a yankin kuma mazaunansa da dama sun bazu cikin daji wadanda har yanzu ba a tantance iya adadin mutanen da ba a gani ba.
Wani wanda lamarin ya faru a idonsa kuma ya bukaci da a sakaya sunansa ya ce shi ma da kyar ya tsira don da idonsa ya ga maharan wadanda ya ce yawansu sun kai 70 dauke da bindigogi akan babura.
Daya daga cikin wanda suka rasa ‘yan uwansa har uku ya shaidawa Muryar Amurka cewa mutanen sun zo sun afka kauyen suka fara harbin kan mai uwa da wabi.
Alhaji Tanko Andami, tsohon ‘dan majalisar dokoki na Jihar Taraba kuma mai fada a ji a yankin da abin ya shafa, ya bukaci da a kawo musu agajin gaggawa a yankin don suna cikin mawuyacin hali.
A lokacin da muke hada wannan rahoton mun nemi mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Taraba SP Usman Abdullah amma ba mu samu nasara ba.