An buga kararrawar hasumiyar agogon “Big Ben”, daya daga cikin alamomin birnin Landan na kasar Ingila, har sau 11 yayin bukin cika shekaru 104 da kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ta kawo karshen Yakin Duniya na daya a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1918.
An buga karrarawar hasumiyar agogon Big Ben, wanda aka sake ginawa kwanan nan a babban birnin Landan, sau 11 a Ranar Armistice don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a yakin da karfe 11:00 agogon gida.
Mutane kuma a duk fadin kasar sun yi shiru na tsawon mintuna biyu a wani bangare na bukin tunawa da cika shekaru 104 da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen kawance da Jamus a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 1918 da karfe 11:00 na safe.
Kusa da Big Ben, an ajiye wani furen girmama mamata a gaban gunkin Mary Seacole da ke Asibitin St. Thomas.