Alkaluman da hukumar kula da kadarorin kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin ta fitar jiya Talata sun nuna cewa, a kaso uku cikin hudu na farkon shekarar 2022, tattalin arzikin manyan kamfanoni mallakar Kasar China na gudana yadda ya kamata, adadin ribar da suka samu ta karu. Gaba daya adadin kudin shigar da suka samu, ya kai kudin Sin yuan triliyan 29, adadin da ya karu da kaso 10.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Alkaluman sun nuna cewa, kamfanoni mallakar gwamnati sun samu ci gaba mai inganci, inda a rubu’i uku na farkon bana, gaba daya adadin kudin da kamfanonin suka kashe a bangaren aikin nazarin kimiyya da fasaha ya karu da kaso 17.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana ribar da suka samu ta kai kaso 7.2 bisa dari, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi.
Hakazalika, adadin harajin da kamfanonin suka biya a wannan wa’adi, ya kai kudin Sin yuan triliyan 2.1, karuwar kaso 15.2 bisa makamancin lokacin bara.