Shugaban Kungiyar Tarayyar Afrika (AfB) kuna Shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya bayyana nahiyar Afrika a matsayin yankin da ya fara zama cibiyar aiyukan taaddanci na Duniya.
Da yake jawabi a wajen taron tattauna wa bisa zaman lafiya da tsaro da aka gudanar a Dakar, babban birnin kasar Senegal, Sall ya ja hankali game da karuwar aiyukan ta’addanci a sassa daban-daban na nahiyar.
Da yake bayyana cewa ta’addanci ya zama matsala a duniya, Sall ya yi nuni da cewa Afrika ta biya babban farashi a wannan fanni.
Shugabannin kasashe, ministoci, jami’an diflomasiyya da wakilan kungiyoyin kasa da kasa da dama ne suka halarci taron na kwanaki biyu.