Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero ya bar Najeriya zuwa kasar Maroko domin halartar bIkin dawaki na kasa da kasa karo na 13 a birnin El-Jadida da ke gabar teku tsakanin 18 ga Oktoba, 2022 zuwa 22 ga Oktoba.
Masu shirya wannan biki ne suka gayyaci Sarkin na Kano a matsayin babban bako a lokacin bikin.
Bikin gargajiyan na hawan dawakin yana amfani da fa’idodi masu yawa wadanda suka hadar da cigaban bunkasar harkar Noma, haɓakawa da adana al’adun gargajiya, muhalli, wasanni a matsayin tushen nishaɗi wanda ke haifar da alaƙar zamantakewa mai ƙarfi.
Buga da kari bikin na wannan shekara zai ƙunshi sabbin abubuwa da dama tare da nishaɗi da al’adu da fasaha da wasanni da gasar wasan dawaki tare da halartar ƙasashen Afirka da yawa.
Tuni dai wata tawaga daga Kano tayi tattaki zuwa Masarautar ta Marocco domin halartar bukukuwan da gasa a yayin bikin.
Alhaji Aminu Ado Bayero CFR yana tare da Alh. Ahmad Ado Bayero Sarkin Dawakin Tsakar Gida da Amb. Ahmed Umar OON Dan Malikin Kano da Mal.Isa Bayero, da sauran ma’aikatan ta Kano.
Ana sa ran dai Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero zai dawo gida
Najeriya a ranar Lahadi 23 ga Oktoba, 2022.
Abubakar Balarabe Kofar Naisa Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano.