Dubban jama’a ne suka fito zanga-zanga a unguwar Dorayi dake jihar Kano bisa nuna adawar su da halayyar nan ta yanka filayen Gwamnati tare da cefanar da su ga masu hanu da shuni a jihar.
Daga B. IMAM
An ga masu zanga-zangar suna daga kwalaye dauke da rubuce-rubuce da suke kira ga gwamnatin jihar ta dakatar da gine-gine da aka fara fitarwa a cikin makarantar.
A nasu bangaren masu gudanar da sana’o i a jikin makarantar sun bayyanawa wakilin Aksammedia yadda abin yazo musu bagatatan kuma aka ce su tashi.
Daya daga cikin masu Sana’a a gurin Yusuf sani yace ance musu su tashi ko kuma su sayi rumfunan da aka yanka akan kudi naira miliyan uku da Rabi 3,500,000 inda yace su talakawa ne basu da hanyar wadannan makudan kudade sai dai idan gwamnati zata shigo tayi musu dashin gata.
Ya Kara da cewa yanzu hakama duk wata suna hada naira 500 suna baiwa hukumar makarantar kuma dasu ake siyan tsintsiya da abin wanke bandakunan makarantar.
Kazalika yace maimako a yanka filin cikin makarantar da yanzu take son gyare-gyare masu yawa amma gara a zo a yi gyaran da ya dace.
Bayan jin ta bakin masu zanga-zangar Mun sami jin ta bakin shugaban karamar hukumar Kumbotso Inda yace ba hurumin su bane na KNUPDA ne bayan tuntubar KANUPDA su kuma suka ce hurumin gidan malamai me daga karshe su kuma sukace ministry of education ne suke da hurumi.
Ku biyo mu Dan jin yadda zata kaya