Yanzu-yanzu INEC ta tantance wadanda za su yi aikin sa Ido a ranar zabe

Wannan na zuwa ne bayan wata ganawa da kungiyoyin sa idon kan zaben da shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ya yi da su, inda ya gargade su da kada su shiga harkokin zabe ko mara wa wata jam’iyya baya.

Yayin da ya rage saura ‘yan kwanaki a gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki a Najeriya, hukumar zabe ma zaman kanta ta Najeriya INEC ta gargadi kungiyoyin sa ido a kan zabe na kasar da na kasa-da-kasa, da su guji nuna goyon baya ga kowace jam’iyya, koma katsalandan kan harkar zabe yayin da suke bakin aiki koma bayan kammala aikin sa ido kan zaben.

Shugaban Hukumar zaben ta Najeriya Farfesa Mahmoud Yakubu ne ya yi wannan gargadi yayin ganawa da kungiyoyin na sa ido kan zabe.

Ya ce hukumar ta tantance tare da bada izini ga kungiyoyin sa ido da ke cikin kasar guda 196 wadanda zasu tura wakilansu 144,800 a lokacin zabe, ya kara da cewa hukumar ta tantance kungiyoyin sa ido na kasa-da-kasa da suka kai 33 wadanda za su tura wakilai 2,113.

A cikin jawabin ya ce “kada ku kuskura ku shiga harkar zabe ko kuma harkokin siyasa da jamiyyu.

Dole ku sani cewa Najeriya kasa ce mai ‘yanci da zata gudanar da zabe don haka ku mutunta wannan ‘yanci na Najeriya.”

Yanzu haka dai yan kasar na zuba ido suga irin rawar da kungiyoyin sa idon na cikin gida da na kasashen waje za su taka a zaben.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments