Man United za ta tsawaita kwantiragin Rashford, Juve na son karɓar Luiz ta bayar da Kean.
Daga Walid Y Hari
Manchester United na shirin tattaunawa da dan kwallon tawagar Ingila, Marcus Rashford, mai shekara 24, kan tsawaita zamansa a club din, bayan da ya fara kakar bana da kafar dama.
Dan wasan Southampton, mai shekara 28 dan kwallon Ingila, Nathan Redmond na dab da zuwa Besiktas domin a auna koshin lafiyarsa a shirin da yake na komawa kungiyar dan cigaba da taka leda kafin a rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a kasar Turkiya a yau Alhamis.
Juventus na shirin yin musaya da dan wasan Aston Villa mai shekara 24 dan kasar Brazil, Douglas Luiz, domin ta bayar da Moise Kean, mai shekara 22, zuwa Ingila da taka leda.
Ana sa ran Luiz zai bar Villa a karshen kakar bana a matakin wanda kwantiraginsa zai kare a kungiyar.
Galatasaray ta amince ta dauki aron dan kwallon Paris St-Germain mai shekara 29 dan kasar Argentine.