An bayyana nada Lamin Sani Zawiyya a matsayin kwamishinan kananan hukumomi na Jihar Kano da cewa abune daya dace a dai dai lokacin da ake bukata.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa daga kungiyar Samarin tijjaniya ta kasa Mai dauke dasa hannun babban Sakataren kungiyar Shehu Tasiu Ishaq da kuma Sakataren yada labarai Abubakar Balarabe Kofar Naisa.
Daga B.imam
Kungiyar samarin tijjaniya tace zabin da Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yayi na bawa lamin sani wannan ma’aikata ya sake tabbatar da cewa gwamnatin Kano tana ajiye kowanne Mai mukami a gurbinsa domin samun daidaito don cigaban Jihar Kano.
A bisa hakan ne kungiyar ta bukaci Sabon kwamishinan kananan hukumomi na Jihar Kano Dr lamin sani Zawiyya yabawa marada kunya ta hanyar cigaba da jajircewa dayin aiki tukuru kamar yadda ya Saba.