Yan sanda sun cafke abokan matashin da ya mutu a wurin Birthday

Wani matashi ɗan shekara 21 a duniya, Micheal Arigbabuwo, ya rasa rayuwarsa a wurin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwa bayan haɗa manyan miyagun kwayoyi da suka sha ƙarfinsa.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta kasa  reshen jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin  a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi.

Hundeyin yace lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta gabata a yankin Ikorodu, dake jihar Legas, kuma ya ƙara da cewa abokanansa uku waɗanda suka halarci wurin sun shiga hannu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments