Duk da cewa Naira ta fara farfadowa daga faduwa da ta yi a cikin makonnin 2 da suka gabata har ta kai ga naira 910 a bisa dala 1 wanda yanzu an sami farfadowa da kaso 20.8, naira ta koma 720 a bisa kowacce dala 1, masana tattalin arziki na ganin salon da aka dauka ne ke karya darajar Nairar.
Alkaluman kididdiga daga kasuwannin canjin bayan fagge na biranen Abuja, Legas, Kano, Fatakwal da dai sauransu, sun yi nuni da cewa farashin dala ya fadi a ‘yan kwanakin nan, lamarin da bai yi tasiri wajen rage tashin farashin kayayyakin masarufi a kasuwannin cikin kasar ba.
‘Yan Najeriyar dai na kokawa a game da yadda ba’a iya samun sauki a bisa farashin kayan abinci a kasuwa ko da an sami sauki a faduwar darajar naira kamar yadda ake gani tun ranar Litinin da ta gabata da naira ta sami karfi a kan dala daga 805 zuwa 720 a yanzu.
Wannan al’amarin ya shafi kama daga iyaye mata, masu kanana da matsakaitan sana’o’i kamar na abinci, sarrafa kujeru da dai sauransu sun bayyana cewa, ‘yan kasa na cikin mawuyacin hali.
Fitacciyar ‘yar kasuwa a fannin abinci da sarrafa kujeru, Laylah ali Othman, ta ce kamata ya yi gwamnatin kasar ta duba batun sa ido a kayyade farashin kayayyakin masarufi.
A dandalin sada zumunta na Tuwita, ‘yan Najeriya na dora alhakin faduwar darajar Naira a kan shugaban babban bankin kasar, Godwin Emefiele inda suke yi masa suka musamman ma bayan da faifan bidiyonsa da ya ke kalubalantar mai kamfanin kasuwar canjin kudi na bayan fagge da ke kayyade farashin canjin dalar Amurka a kan naira wato Aboki FX, da ake ganin kamfanın yake sanadın tashin farashin dala a Najeriya.
Mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mal. Baba Yusuf, ya ce salon tattalin arzikin da Najeriya ta dauka ne babban kalubale da ke karya lagon darajar kudin kasar wato naira, har yake shafar dukannin ‘yan kasar ciki har da talakwa.
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta babban bankin CBN ta fara daukan matakai da take ganin zasu taimaka wajen farfado da tattalin arzikinta da kuma daga darajar Naira kamar sauya launin kudaddenta wato naira 200, 500 da dubu 1.
Sai dai shugaban kungiyar masu gudanar da ayyukan canji na Najeriya, Aminu Gwadabe, ya bayyanawa manema labarai cewa sake fasalin kudin naira ne ya sa ake fuskantar hauhawar farashin dala musamman a cikin makonni biyu da suka gabata.