Babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja ta rushe zaben fdda gwani da jam’iyyar APC ta yi na dan takarar gwamnan jihar Taraba.
Da yake yanke hukunci a ranar Litinin, mai shari’a Obiara Afuegwa Egwualin, ya ba da umarnin a sake wani zaben cikin kwanaki 14 masu zuwa.
A cewar Alkalin, ba a bi ka’ida ba wajen gudanar da zaben Sanata Emmanuel Bwacha wanda aka ayyana a matsayin wanda ya lashe zaben fitar gwanin.
Kotun har ila yau ta ba da umarni ga Bwacha, da ya daina ayyana kansa a matsayin dan takarar gwamna karkashin tutar jam’iyyar APC na jihar Taraba.
Sanata Yusuf A. Yusuf na daya daga cikin ‘yan takarar da ya ruga kotu don a bi masa kadi inda ya ce, ba a yi zaben fitar da gwani na kujerar gwamna a jihar ba.
A nasu bangaren, wasu daga cikin mazauna jihar Taraba irinsu Alhaji Abubakar Naira, cewa suka yi wannan al’amarin ya yi, domin dama an take ka’idojin dimokradiyya.
Su kuwa bangaren Bwacha ta bakin mai magana da yawunsa Ambasado Rikwense Muri, ya ce suna da daman daukaka kara ko kuma su shiga zaben.