Yan majalisar dokokin Zambia maza sun tilasta wa ministar lafiya ta kasar wadda ita ma ‘yar majalisar ce rufe jikinta bayan da wsu suka yi korafin cewa tana tayar musu da hankali.Dole ta yafa mayafi inda ta rufe kafadarta da bayanta
Ana tsakar zaman majalisa ne sai wani daga cikin ‘yan majalisar na bangaren hamayya ya gabatar da korafi ga shugaban majalisar cewa kayan da takwarar tasu ta sa sun hana maza sakat, suna ja musu hankali.
Daga nan ne sai Shugaban Majalisar Mulenga Fube ya jefa tambaya cewa ko tufafin da Ms Masebo ta sa sun dace ko ba su dace ba, kasancewar ba su rufe bayanta ba sosai.
Rigar da ta sa dai ta rufe kafadarta da kirjinta amma kuma ana iya ganin bayanta kusan a fili fayau.
Duk da cewa shugaban ya ce shi kam bai g wani abu na rashin dacewa da rigar ‘yar majalisar ba, to amma ya bukace ta da ta rufe bayan nata saboda korafin da mazan ke yi.
Daga nan ne Ms Masebo ta aro mayafi daga wata ‘yar majalisar ta yafa kafin daga baya ta je ta samo nata ta rufe jikin nata.
Masu rajin kare hakkin jama’a sun kira lamarin da wariya, inda Mirriam Mwiinga ta kungiyar Kiristoci ta matasa mata ta kasar ta gaya wa BBC cewa lamarin ya nuna wariya ga mata kuma bai tabbatar da ‘yancin da y kamata a ce mata suna da shi ba
Su dai ‘yan majalisar dokokin kasar ta Zambia a lokacin zaman majalisa akwai kayan da ya kamata su sa, wadanda s uke nuna kamala.