Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa ta rundunar ta Operation Hadin Kai, sun kashe ‘yan tada-ƙayar baya na Boko Haram 31 da kuma na ƙungiyar ISWAP ta Yammacin Afrika tare kuma da kama wasu 70 a arewa maso gabashin Najeriya.
Darektan ƴada labaru na hedkwatar tsaron ƙasar, Manjo Janar, Musa Danmadami ne ya bayyana hakan yau a Abuja yayin taron manema labarai kan nasarori da sojojin ƙasar suka samu a makonni biyu da suka gabata.
Danmadami ya kara da cewa mutum 70 daga cikin wadanda ta kama a yankin arewa maso gabas, 60 daga cikinsu sun kasance suna samar wa da ‘yan tada-ƙayar bayan kayaki kamar abinci da makamai da man fetur da sauransuy.
Mai magana da hedkwatar tsraon ta Najeriya, ya ce dakarun ƙasar sun samu nasarar ceto mutum biyu da aka tsare, inda ‘yan tada-ƙayar baya 366 tare da iyalansu suka miƙa wuya.
Har ila yau, Danmadami ya ce a ranar 11 ga watan Oktoba ne, sojoji suka yi wa ‘yan ta’adda kwantan bauna a Bama da Ngala wanda ya kai mutuwar 18 daga cikinsu yayin da wasu suka tsere, inda akakwato makamai da dama.
Manjo Janar Musa ya kuma ce cikin makaman da aka kwato sun hada da bindigar AK-47 guda ɓiyar da bindigar M21 da buhunan wake 64 da na shinkafa ɓiyar da magunguna da kayan sawa da ƙananan dabbobi da kudi naira 250,000 da da babura 11 da kekuna ɓiyar da sauransu.