Wata jaririya ta rasu bayan da wani rakumin dawa ya tattake ta a wani gandun namun daji a Afirka ta kudu yayin da mahaifiyar jaririyar ke asibiti cikin mawuyacin hali.
Jaririyar ‘yar wata 16 tana tare ne da mahaifiyarta a wani daga cikin gidaje na alfarma da ke gandun daji na Kuleni Game Park a lardin KwaZulu-Natal.
‘Yan-sanda sun gaya wa manema labarai cewa har yanzu babu cikakken bayani kan yadda lamarin ya faru, amma dai sun fara gudanar da bincike.
Ba abu ne da aka saba gani ba rakumin dawa wanda kusan ga shi nan da yawa a gidajen namun daji da gandun daji a Afirka ta Kudu, ya far ma mutane.
Jami’in ‘yan-sanda Laftana Nqobile Madlala ya gaya wa yan jarida cewa faruwar abin ke da wuya aka garzaya da uwar da jaririyarta zuwa dakin likita da ke kusa inda a can jaririyar ta rasu.
Ba a dai san takamaimai inda abin ya faru ba a jiya Laraba, a babban gandun wanda yake da masaukin baki na alfarma har guda 14.
Rakumin dawa shi ne dabba mai shayar da nono mafi tsawo a duniya, kuma ba dabba ce da aka sani da fada ba.