Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi ta samu tun cikin makwanni biyu a kasar Africa ta kudu ya haifar da lalacewar gidaje da hanyoyi, lamarin da ya yi sandiyyar rasuwar mutane 16, a birnin Johannesburg na na kasar.
Yayin zantawa da manema labarai game da hakan a jiya Asabar, mai rike da mukamin magajin garin birnin mafi girma a Afirka ta kudu, uwargida Mpho Phalatse, ta ce sakamakon ayyukan ceto da ‘yan sanda ke gudanarwa, an yi nasarar ceto rayukan mutane 148.
Baya ga gidaje da hanyoyi, ruwan saman kamar da bakin kwarya, ya kuma lalata muhimman ababen more rayuwar jama’a, kamar fitilun ba da hannu dake tituna, da tashoshin samar da lantarki da bututai, tare da hallaka dabbobi da tsirrai masu tarin yawa