Daga Sadik Lamin Hassan
Majalisar wakilan Nigeria ta ce ba zata sabu ba Bindiga a ruwa, ba zasu yarda ba, suna bukatar a ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗaɗen Naira (N1000, N500, N200) domin hakan ba zai kawo maslaha mai kyau ba.
Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Tarauni daga jihar Kano, Hafizu Kawu, ne ya bayyana haka a yau.