Yadda taron wayar da kan mata alfanun zaman lafiya na Gidauniyar CARDINAL ONAIYEKAN ya gudana

Anyi kira ga matan jihar Kano daga dukkan addinai dasu taka rawar da ta dace a zabukan dake tafe.

Kiran ya fito ne daga cibiyar Samar da zaman lafiya a tsakankanin mabiya addinai ta Cardinal ONAIYEKAN FOUNDATION a taron  da ta jagoranta yayin  bayar da horo ga mata dari akan yadda zasu Samar da kyakyawan jagoranci akan mazajensu da ya’yansu

Wakiliyar cibiyar da tazo daga Abuja Mrs Augustiner Richard tace iyaye musamman mata suna da damar dakile  tayar da tarzoma a kafin da lokutan zabe don kaucewa fadawar ya’yansu cikin matsala.

Mrs Augustiner tace wannan fadakarwa suna sa ran zata yadu a sassan jihar Kano musamman ga wakilcin Addinin musulumci Dana kiristanci baki daya.

Hajiya salamatu Ibrahim daya daga cikin mashirya Shirin fadakarwar ta wuni guda ta bayyana cewa zasuci gaba da yin duk maiyiwuwa wajen ganin tarbiyyar mata ta inganta domin sune ke rike da ragamar mazajensu da kuma ya’yan su musamman matasan da sukafi tasiri wajen tayar da tarzoma ganin sunyi abin daya dace don dakile lalacewar wadanda suke jagoranta.

A jawabansu daban daban wakilan kungiyoyin Addinin musulumci dana kiristanci malama Maryam da kuma Mrs Kifkatu sun kira ga mahalatta taron dasubi hanyoyin zaman lafiya domin tarbiyantar da ya’yansu da zama da makwaftansu da suke mabambantan addinai da kuma yare lafiya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments