Yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace yara kanana 20 inda suka nemi N40 miliyan na kudin fansa.
An gane cewa sun kwashe yaran da suka hada da mata 16 sai yara maza hudu tun kwanakin baya a yankin Kusherki dake karamar hukumar Rafi
Mazauna yankin da iyayen yaran suna neman daukin hukumomi sakamakon labarin azabtar da yaran da aka gano ‘yan bindigan suna yi