Shugaban Hukumar RMAFC ya tsaya tsayin-daka a kan cewa sai an yi wa wasu jami’ai karin albashi
Mohammed Shehu yace sun dauki matakin ne saboda akwai ma’aikatan da sun fi shugaban kasa albashi
RMFAC tace albashin shugabannin irinsu NPA, NCC da Gwamnan CBN ya zarce na Muhammadu Buhari
Hukumar RMAFC mai alhakin yanke albashin ma’aikata da ‘yan siyasa a Najeriya, ta dage a kan batun yin karin albashin ga ‘yan siyasa.
This Day tace shugaban RMAFC na kasa, Mohammed Shehu ya kare matakin nan da suka dauka, yace bai dace wani ya fi shugaban kasa albashi ba.
Shehu ya ambaci hukumomi da cibiyoyin gwamnati irinsu NCC mai kula da harkar sadarwa da babban bankin CBN a cikin masu albashi mai tsoka.
Kazalika yace jami’an hukumar NPA mai kula da tashohin ruwa, su na tashi da kudin da ya zarce samun Mai girma shugaban kasar Najeriya.
Shehu yana cewa hukumomin da ke tatsowa gwamnatin Najeriya kudin shiga, sun fi sauran takwarorinsu albashi saboda a hana su sata.
Da aka zanta da shi a gidan talabijin na Channels, shugaban na RMFAC ya bayyana cewa akwai matsala a game da tsarin albashin kasar.