Kungiyar masu Samar da zaman lafiya da yin sulhu tsakanin mabiya addinai sun Kai ziyara ga hukumar kare haqqin dan’adam ta kasa da kasa kuma shugaban makarantar koyar da kare hakkin Dan Adam karkashin jagoranci Ambasada Tijjani shehu Idris da wata wata cibiya Mai Samar da aikinyi ga matasa. Malam Nuhu Muhd shugaban kungiyar Samar da zaman lafiya ta CMMRC yace kudirin kungiyar shine su yada mahimmanci zaman lafiya , yace a yanzu haka sun shirya tsaf don dakile fadace fadacen makiyaya da manoma dake fadin Kano da makwaftanta. Ambasada Tijjani shehu Idris ya yaba da ayyukan CMMRC inda yace su fadada ayyukansu su game fadin kasar nan ta yadda zasuyi magana da murya daya kamar yadda hukumar tasu take wajen yin aiki da ga ko ina a fadin duniya tare da bayyana fara aikin sabuwar makarantar horas da kare hakkin don Adam a bisa tsari . Ambasada Tijjani shehu Idris ya tallafawa kungiyar da kudi dubu dari domin su ci gaba da taimakawa mabukata.A nasa bangaren shugaban cibiyar hada magunguna da samawa matasa aikin yi Dr Nura Adam salihannur ya CE zasu yi tafiya a tare da kungiyar ta CMMRC domin irin ayyukan su daya.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya naɗa sabbin shugabanin hukumomin NIA da DSS
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar tsaron kasa ta NIA, ya yin...
Read more