Hukumar hisbah ta jihar Kano ta ja hankalin kungiyoyin mata da suke rajin kare haqqin mata da yara dasu kaucewa bin diddigin laifukan maza da nufin kawo karshen cin zarafin mata da yara .mataimakiyar kwsmandan hukumar a bangaren mata Dr Khadija sagir sulaiman ita ce tayi wannan Kiran a Yayin ziyarar da kungiyar kare haqqin mata da yara ta Baubab ta kawo musu ziyara ofishin hukumar hisbah dake sharada tace muddin kungiyar ta na son a fahimci manufarta to babu shakka sai ta kiyaye da fifita mata akan maza domin a zauna lafiya sannan su fi bayar da karfi wajen ganin matan sun gyara dabi’unsu kamar yadda mahalicci yace mata da mazan suyi mu,Amala da kyautatawa a tsakaminsu. Itama a nata bangaren shugabar kungiyar kare haqqin mata da yara ta Boubab Hajiya zubaidah Ahmad Nagi tace su kawo ziyarar ne domin neman goyon bayan hukumar hisbah ta furkar kawo karshen cin zarafin mata da yara da wasu dai daikun maza kanyi tare da bayyana irin ayyukan da sukeyi domin tallafawa rayuwar mata da yara.dr Khadija sagir sulaiman ta Kara jaddada musu dasu bawa gyaran tarbiyyar matan fifiko.
Yanzu-yanzu: Tinubu ya naɗa sabbin shugabanin hukumomin NIA da DSS
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Ambasada Mohammed Mohammed a matsayin sabon shugaban hukumar tsaron kasa ta NIA, ya yin...
Read more