Shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso, Laftanar Kanar Paul Henri Sandaogo Damiba da aka hambarar a ranar juma’ar da ta gabata, ya amince ya sauka daga mukamin sa sakamakon shiga tsakanin da shugabannin addini suka yi.
Sanarwar da shugabannin addinan kasar suka gabatar tace Damiba da kansa ya amince ya sauka daga shugabancin kasar domin kaucewa zubar da jini.
Rahotanni sun ce yau sai da jami’an tsaro suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga zanga kusa da ofishin jakadancin Faransa, saboda zargin da akewa kasar na goyan bayan hambararren shugaban.
A jiya asabar Damiba da aka ruwaito ya samu mafaka a tsohon sansanin sojin Faransa yace ba zai sauka daga mukaminsa ba, yayin da ya bukaci kananan sojin da sukayi juyin mulkin da su koma bariki domin tattaunawa.
Yau tarin magoya bayan sabon shugaban sojin Ibrahim Traore sukayi gangami a kusa da ofishin jakadancin, yayin da Faransa tayi Allah wadai da tashin hankali kusa da ofishinta.
Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun lalata Cibiyar Faransa dake Bobo-Diolasso da kuma Ouagadougou.