Barayin da suka saci mota ana huduba sun shiga hanun yansanda

Babban malami Salihu S. Abubakar shi ne ya jagoranci sallar juma’a a ranar kuma ya gabatar da hudubar ranar a kan jin tsoron Allah da rungumar kyawawan halaye.

Sai dai a Iya cewa wasu daga cikin masu sauraron hudubar ba Sallami ce ta kaisu masallcin ba tunda bayan idar da sallar aka nemi motar limamin kirar Hilux, aka rasa, karshe sai dai shehin malamin ya koma gidansa dake Zango a wata motar dabam.

Nan take aka bazama sanar da jama’a da hukuma kan abinda ya faru. Kuma wannan labari ya karade shafuka da dandalin sada zumunta tun a lokacin.

Wani malamin jami’a, Dr. Mustapha Auwal Imam yana cikin wadanda suka bada sanarwa a Facebook, wanda wannan ya sa labarin ya karade wurare da yawa.

Kawo Yanzu cikin huwacewar buwayi an Sami nasarar gano motar kamar yadda jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano  Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar.

Kiyawa yace sun yi ram da mutane biyu da ake zargi da laifin satar, ya kuma bada lambar da masu motar za su tuntube shi.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments