Gwamnatin kasar Ghana ta koka da yadda ta dauki lokaci mai tsawo tana kaddamar da tsare-tsare wadanda suke mayar da hankali wurin kara habaka bangaren samar da kifi, amma kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu
A cewar shugaban kasar ta Ghana Nana Akuffo-Ado su kirkiri shiri mai suna ‘Aquaculture for Fish and Jobs’.
Wannan shirin an kaddamar da shi ne a 2018 domin samar da kayayyakin noman kifi ga manoma domin habaka kiwon kifi.
Mataimakin ministan kiwon kifi Moses Anim ya bayyana cewa gwamnatin kasar na kokarin kara karfin gwiwa domin habaka samar da kifi a cikin kasar ta hanyar hana masu son shigar da kifi cikin kasar kudin kasar waje domin kasuwanci.
Amma Jennifer Sodji, shugaban kungiyar masu kiwon kifi ta Ghana yana ganin cewa akwai bukatar gwamnatin Ghana ta kara kokari.
Akwai bukatar hukumomi “su rage haraji a bangaren” domin rage tsadar abincin kifi wanda akasari shigar da shi kasar ake yi, kamar yadda Sodji ta shaida wa TRT Afrika.
Ta bayyana cewa “bayar da tallafi ga manoman kifi” zai taimaka kiwonsu ya bunkasa” domin samar da kifin a cikin kasar.
“Ina ganin za mu iya yin abubuwa da dama a wannan bangaren” kamar yadda ta bayyana.