Makarantar Darul khair waddarasatil islamiyya ta gudanar da saukar dalibanta Karo na farko tare da kaddamar da gidauniyar taimakawa makarantar.
Malama Iklima Awwal Saleh shugabar makarantar tayi kira ga al’umma dasu kara zage damtse wajen tallafawa marayu a unguwanninsu domin dimbin ladan da hakan ke dashi tare da samun tsira a gobe kiyama.
Malamar tace mafi rinjayen daliban makarantar darulkhair islamiyya marayu na da makarantar da wasu bayin Allah masu taimako suke daukan nauyin karatunsu don haka take Jan hankalin bayin Allah masu son dacewa dasu tallafawa marayun don ganin sun zama daidai da sauran yara masu iyaye a Raye.
Shugabar makarantar tace a saukar qur’anin makarantar karo na farko sun yaye dalibai 10 a madadin goma sha daya da aka tsara sakamakon wani dalibi guda da yarasa ransa kafin saukar
Daga karshe ta godewa mahalatta taron da wadanda suka bayar da gudimmawar su ga makarantar don ganin ta bunkasa
Wasu dalibai da muka zanta dasu Ibrahim da Aisha sun nuna Jin dadinsu da mahalicci ya kaddara suka ga wannan rana da ba zasu manta da it’a ba a tarihin rayuwarsu