Dubban mutane ne suka nemi amsan rainon jaririyar da aka haifa a karkashin baraguzai a kasar Siriya bayan girgizar kasar da ta afku a Kahramanmaras a ranar 6 ga watan Fabrairu.
Igiyar cibiyar jaririyar mai suna Aya (abun al’ajabi) da aka haifa a karkashin baraguzai a garin Cinderes da ke Afrin, na hade da mahaifiyarta da ta rasu, a lokacin da aka ceto ta.
Mahaifiyarta, mahaifinta da ‘yan uwanta 4 da suka makale a karkashin baraguzan gininsu duk sun rasa rayukansu.
A halin yanzu Aya tana asibiti.
Dakta Hani Marouf, likitan yara da ya kula da jaririyar, ya ce jaririyar na cikin mawuyacin hali lokacin da aka kawo ta asibiti a ranar Litinin da ta gabata, kuma a yanzu haka tana cikin koshin lafiya.
Bidiyon da aka dauka lokacin da aka ceto Aya ya yi tashe a shafukan sada zumunta. Bidiyon ya nuna lokacin da wani mutum ya zakulo jaririyar rufe da kura daga karkashin baraguzai.
Halil al-Suvaydi, wani dan danginta ya kai Aya asibiti a Afrin bayan da aka ciro ta daga karkashin baraguzai.
Dubban mutane a shafukan sada zumunta na tambayar yadda za su iya amsan rainon jaririyar.
Manajan Asibitin, Dakta Attiah Khalid ya bayyana cewa ya samu kiraye-kirayen mutane daga ko’ina a sassan duniya da ke son amsan rainon Aya.
Khalid, wanda ya ke da jaririya da ta girmi Aya da watanni 4, ya ce, “Ba zan bari kowa ya dauke ta ba a yanzu. Zan kula da ita kamar ‘yata har sai danginta sun zo.”
A garin Aya da ke Cinderes, har yanzu mutane na ci gaba da neman ‘yan uwansu a karkashin baraguzan gine-gine.
Mohammed al-Adnan, wani dan jarida a garin ya shaida wa BBC cewa, “Al’amarin yana da muni, akwai mutane da yawa a karkashin baraguzan gine-gine. Har yanzu an kasa fitar da su.”