Rahotanni na nuni da cewa wasu mutane 11 da suka hadar da sojoji da fararen hula sun rasa rayukan su yayin wani harin kwantan bauna da aka kai wani sansanin soji dake arewa maso yammacin Burkina Faso.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa manema labarai cewa, wasu mutane dauke da makamai ne suka kai hari kan sansanin soji a kauyen Zaba dake lardin Nayala na arewa maso yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sojoji 11 da fararen hula masu taimaka musu.
Majiyar ta kara da cewa, harin ya kuma jikkata wasu sojojin da fararen hula. Tana mai cewa an kuma hallaka ’yan ta’adda wajen 20 wadanda suka kai harin.
Kamfanin dillancin labarai na kasar AIB, ya ruwaito a jiya Litinin cewa, an kashe gomman ’yan ta’adda cikinsu har da shugabanni a ranar Lahadi, yayin wani hari ta sama da aka kai musu a yankin gabashi da arewa maso tsakiyar Burkina Faso