Daga Abdulhamid isah D/Z
An yi kira ga daukacin daliban jihar kano da suyi amfani da kudaden tallafin da gomnatin jihar ta basu ta hanyar da tadace
Lawan Yusuf sale sakataran kwamatin kula da ba yara tallafin kuma tsohon shugaban karamar hukumar Gyaya shi ne yayi kiran a zantawar sa da yan jaridu bayan tantance daliban a makarantar Yusuf mai tama sule da aka fi Sani da northwest university.
Kana ya yaba da kokarin Gomnatin jihar kano dangane da raba tallafin duba da yadda a ke fama da karancin kudade a hannun mutane a wananan lokaci.
Hakaza lika ya yayawa daukacin daliban jihar kano da suka basu gagarumar gudummawa wajen gudanar da wananan aiki mai matukar amfani a wajen dalibai.
Sannan ya kara da cewa wananan tantan cewa ya shafi duk wani dalibi Wanda yake karatu a wajen wananan jihar ta kano.
Kakazali ka kusan duk Wanda sukayiwa tantancewar babu jimawa yake jin kudade a cikin asusun bankinsa babu wani tangarda. Domin suma su amfani wananan tallafi kai tsaye daga gomnatin kadimul Islam Dar Abdullahi Umar ganduje
.