Kimanin Mutane sun rasa rayukansu sakamakon guguwar Cheneso da ta yi tasiri a Madagascar.
A cikin sanarwar da Ofishin kula da bala’o’i ya fitar, an bayyana cewa guguwar Cheneso mai zafi da ta shigo kasar daga gabar tekun arewa maso gabas a ranar 19 ga watan Janairu ta yi tasiri a yankuna 8.
A cikin sanarwar, an yi nuni da cewa mutane dubu 13 da 180 ne guguwar ta shafa sannan gidaje dubu 4 da kadada 600 na karkashin ruwa.
Sanarwar ta bayyana cewa mutane 3 ne suka rasa rayukansu a sanadiyyar guguwar kuma makarantu 80 ne suka zama marasa amfani sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku.
Lokacin damina a kasar Madagaska, tsibiri da ke gabar tekun Indiya, na ci gaba har zuwa watan Afrilu.
A bara, guguwa mai zafi 3 da mahaukaciyar guguwa 2 sun yi tasiri a kasar.