Yadda taron gaggawa na jam’iyar APC ya gudana tare da Ministan sharia Abubakar Malami.
A jiya ne jam’iyar APC mai mulkin Najeriya ta kira taron gaggawa da ya hadar da gwamnoni uku da shugaban jam’iyya da kuma Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnati Abubakar Malami
Gwamnonin sun hadar da gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai sai gwamnan jihar Kogi Yahya Bello da gwamnan jihar Zamfara Bello Matawall
Yayi taron gwamnonin sun bukaci gwamnatin tarayya da ta mutunta umarnin kotu akan maganar daina amfani da takardun Naira 500 da 1000.