Ranar matasa ta duniya Rana CE da ake tuna irin gudummawar da matasa suke bayarwa a tsakanin al’umma tare da kasantuwarsu masu maye gurbin shugabanni.Hakan yasa sarkin Fadar kano Hakimin Tarauni Alhaji Ado kurawa ya yabawa gamayyar kungiyoyin matasan karamar hukumar Tarauni karkashin kwamaret Jamilu Wada ta yadda suka Kai agajin gyaran makabartun yankinsu.
AlhaJi Ado kurawa yace fatansu shine matasan jihar Kano baki daya su yi koyi wanna aikin Alkhairin a daukakin kananan hukumomin Kano arba’in da hudu duba da yadda ake samun bata gari suna fakewa da rashin tsaron da ake samu a makabartu na tono bayin Allah da suka rigayemu gidan gaskiya su kuma yanki wani sashen jikinsu domin nemaan duniya.
Yace yin gyaran makabartun zai taimaka matuka .
A na sa jawabin shugaban karamar hukumar TARAUNI Alhaji Abubakar zakari Muhd HABu P A ya cee matasan karamar hukumar sun cancanci yaba bisa wannan abin alkhairi na gyaran makabartun a wani yanki na ranar Sha biyu ga wataAn Agusta matsayin ranar matasa ta duniya Wanda suka amfani ranar da aikin ceton da ya shafi rayayyu da kuma mamata domin dukkan mairai nanne masaukinsa indan Mai aukuwa ta auku.
Shugaban gamayyar kungiyoyin kwamaret Jamilu Wada yace sunyi aikin gayya a makabartu shida dake yankin. Karamar hukumar TARAUNIn domin kawo karshen masifun da suke afkawa makabartun..